Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babban aikin matarsa shi ne dafa abinci, bayan da ta ce ba za ta sake mara masa baya ba idan har bai sauya salon gwamnatinsa ba.
Shugaban, wanda ke ziyara a Jamus, ya mayar da martanin ne cikin nishadi inda ya kwashe da dariya bayan da aka yi masa tambaya kan hirar da mai dakinsa ta yi da BBC.
Ya kara cewa, "Ban san jam'iyyar da matata take ciki ba, amma na sani cewa babban aikinta shi ne dafa min abinci da kuma kula da dakunana."
Wannan ne dai karo na farko da shugaban ke mayar da martani ga matarsa tun bayan da aka fara ce-ce-ku-ce a kasar kan sukar da ta yi wa salon mulkinsa.
Mista Buhari ya ce "na fi ta da kuma sauran 'yan adawa yadda ake tafiyar da gwamnati".
Ita dai uwargidan shugaban na Najeriya ta gargadi mijinta cewa ba za ta goyi bayan takararsa a 2019 ba idan har al'amura suka ci gaba da tafiya a haka.
"Bai gaya min cewa zai tsaya ko ba zai tsaya ba tukunna, amma na yanke shawara a matsayina na matarsa, cewa idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka, to ba zan shiga cikin tafiyar ba.
"Idan har abubuwa ba su sauya ba, to ba zan fita na yi yakin neman zabe kamar yadda na yi a baya ba. Ba zan sake yi ba".
Za ku iya sauraran hirar da ta yi wannan bayani da sauran muhimman abubuwan da ta fada a shirinmu na Ganemi Mini Hanya a ranar Asabar.
Ta ce shugaban bai san mafi yawan mutanen da ya nada a cikin gwamnatinsa ba.
Ta kara da cewa wasu "'yan tsiraru" ne suke juya akalar gwamnati, inda suke zabar mutanen da ake bai wa mukami.
0 Comments: