Monday, 22 January 2018




Kiwon Lafiya: Amfanin Madara Ajikin Fatan Dan Adam

Home Kiwon Lafiya: Amfanin Madara Ajikin Fatan Dan Adam

Post By:

Ku Tura A Social Media
Kiwon Lafiya: Amfanin Madara Ajikin Fatan Dan Adam

Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan fili na kwalliya. Madara na dauke da sinadaren da ke saurin gyara fata.

 Yawan bai wa yara madara na dada kaifin basira ga yaro. Bayan haka, shan madara na sanya fata sulbi da laushe da kuma kare fata daga gautsi.

• A sami madara sannan a kwaba ayaba. A zuba ruwan madarar da ayabar ta dan yi kauri kadan sannan a rika shafawa a fuska na tsawon minti goma sha biyar a rana sannan a wanke. Yin hakan na sanya sulbin fuska.

A sami madaran gari sannan a kwaba shi da ruwa sannan a matse ruwan lemun tsami a ciki sannan a gauraya a rika shafawa a fuska kafin a shiga wanka a kullum domin samun hasken fata.

• Madara na goge dukanin daudar fuskar; za a iya samin rabin kofin madara sannan a hada ta da rabin cokalin gishiri sai a sanya ruwa a gauraya har sai gishirin ya narke.

Bayan hakan, sai a shafa a fuska da wuya a jira na tsawon minti 2 zuwa 3 kafin a wanke da ruwan dumi.

• Madara na sanya fata sulbi domin hakane ya kamata a rika amfani da shi a matsayin cleanser ; a samo auduga sannan sai a tsoma a cikin madarar ruwa. Sai a rika goge fuskar da ita, sannan sai a jira ta bushe kafin a wanke, yin hakan na rage maikon
fuska kuma da sanya fuska taushi da sulbi.

• Za a iya amfani da madara a gashi domin kara wa gashi lafiya. Musamman lokacin sanyi, gashi .

Sai a zuba madara a gashi ya taba tsagun kai, sai a jira na dan minti kadan kafin a wanke. Yin hakan na kara karfin gashi kuma yana hana shi tsinkewa.

Za a iya hada madara da zuma sannan a shafa a fuska. Yin hakan na hana fashewar fuska saboda sanyi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: