An Dakatar Da Jami’an Hukumar JAMB Da Suka Yiwa Maciji Kazafin Hadiye Milyan 36
Hukumar Shirya jarrabawar shiga jami’a wato, JAMB ta dakatar da duk jami’anta da ke da hannun wajen bacewar Naira milyan 36 na kudaden cinikin katin jarrabawar shiga jami’a a jihar Binuwai.
Jami’in Yada Labarai na hukumar, Fabian Benjamin ya ce, an fara bincike kan yadda kudaden suka salwanta bayan da jami’an suka yi wa wani maciji kazafin cewa ya shiga ofishin da aka adana kudaden ya hadiye su.
#RARIYA
0 Comments: