Rahama Sadau Ta Bayyana Wanda Take So
Tauraruwar fina-finan Hausa, da turanci, Rahama Sadau ta bayyana abokin aikinta na fim din turanci, Alexx Ekubo a matsayin wanda take muradi/ take so, Rahamar ta bayyana hakanne a dandalinta na sada zumunta da muhawara.
A wannan hoton na sama Rahamar ce tare da Alexx din. Rahamar dai a kwanakin baya ta bayyana cewa tana son shahararren dan kwallo Neymar da kuma abokin aikinta mawaki Umar M. Shareef.
0 Comments: