Wani taron taurarin fina-finai mata na Duniya da aka gudanar a kasar Amurka, da tauraruwar fina-finan Hausa da turanci Rahama Sadau ta samu halarta yayi mata armashi domin kuwa an bata lambar girmamawa a gurin taron.
Da take bayyana farin cikinta akan wannan lamari Rahama Sadau tace taji dadin halartar wannan taro kuma ta hadu da manyan mata daban-daban, haka kuma ta kara da cewa akwai lokacin da a rayuwa zaka tsaya ka tambayi kanka wai yaushe har nakai matsayin da nike?, tace to tayi irin wannan tunani akan wannan taro kuma ba zata taba mantawa dashi ba.
Muna tayata murna.
0 Comments: