Shugaba Buhari ya bayyana cewa babu gaskiya a zarge-zargen da wasu keyi na cewa yana nuna banbancin addini a gwamnatinshi, ya bayyana hakane lokacin da ya gana da kungiyar limaman kiristocin Arewa da suka kaimai ziyara fadarshi.
Yace tunda yake a aikin soja da kuma sauran mukamai da ya rike, be taba sabawa dokar aikinshiba, koda lokacin da ya shugabanci kasarnan karkashin mulkin soja, majalisar zartarwa ta wancan lokacin tana kunshe da mafi yawancin kiristane kuma yakan yi amfani da kwarewa da cancanta wajan bayar da mukamai.
Shugaba Buhari a cikin sanarwar da me magana da yawunshi, Femi Adesina ya fitar ya kara da cewa, ko da gwamnatinshi ta yanzu kuwa kowane bangare nada wakilci daidai da daidai a cikin majalisar zartarwa, dan haka baya nuna banbanci.
Shugaba Buhari ya kara da kiran shuwagabannin addini da su rika bayar da gudummuwa wajan habaka hadin kai da zaman lafiya tsakanin mutane, haka kuma ya amince da shirin kungiyar kiristocin na shirya wani taro dan yiwa kasa addu'a da kuma yin azumin rana daya dan cigaban kasarnan.
0 Comments: