Illolin Hassada Da Maganinta - Dr Jabir Sani Maihula
1) Hassada shine mutum yaji zafin wata ni'ima da Allah yayiwa wani bawan sa, koda baiyi fatar gushewar ni'imar ba. [Ibn Taymiyya da wasu malamai]
2) Hassada halin yahudawa ce [ Qur'an 2: 109, 4:54, 48:15]
3) Hassada tana kama wanda akayiwa ita, komai imanin sa; ta kama Annabi Yusuf (A.S), kuma Allah ya umurci Annabi (S.A.W) daya nemi tasri daga sharrin mai hassada [Qur'an 113:5].
4) Karanta azkar na safe da yamma, da karanta Fatiha, da karshen suratul Bakara, da ayatul Kursiy da suratul Falaq da Nas ya na kariya da ga hassada da bala'oi [hadissai da yawa]
5) Boye ni'ima ga wadan da ka ke tsammanin zasuyi ma hassada yana kareka daga hasada ya yardar Allah [quran 12:5].
6) Annabi (S.A.W.) yahana hasada, cikin hadissai dayawa cikin su akwai [ Muslim 2559]
7) Mai hassada yana fada ne da Allah, domin Allah shi yake yin ni'ima ga wanda yaga dama, kuma Allah shiyafi sanin wanda ya cancanta. [Malamai]
8) Mai hassada kullum yana cikin bakin ciki da bacin rai wanda ba lada akai [ laa tahzan, A'ed alQarny].
9) Hadisin da ya shahara na "Hasada tana cin ayyukkan..." bai inganta ba.
10) Allah yayi mana tsari daga hassada, yasa kada muyiwa wani, kuma ya tsare mu daga masu yi mana.
0 Comments: