Friday, 6 April 2018




Kannywood: Shararriyar jaruma Maryam Booth ta rabawa marayu kayan sallah

Home Kannywood: Shararriyar jaruma Maryam Booth ta rabawa marayu kayan sallah

Post By:

Ku Tura A Social Media
             
  Image © Mujallarmu.Com

Jaruma Maryam Booth tayi rabon kayan sallah ga marayu kananun yara maza da mata a Nasarawa dake kano,jarumar ta raba shaddoji da yadika masu din ki da ado na zamani.

Dandalin Arewafresh.com ta samu labarin cewa awajen rabon ne wakiliyar majiyar mu Maryam Hotoro ta sami sukunin

 zantawa da jarumar kamar haka:
Maryam kin rabawa marayu kayan sawa, kuma da alamu wadan nan yara marayune, wanne hange ki kayi wanda yasa ki ka rabawa marayu kayan sallah amadadin ki ba masu iyaye? Wannan

 tambaya tana da saukin amsawa.
Domin amsarta yana cikin tambayarki. Duk yaron yake da iyaye to tabbas yana da tabbacin samin kayan sallah, amma maraya bashi da tabbas.

Dan haka naga gwara in ba marayu zaifi kyautuwa.

Me za kice da yan uwanki jarumai akan irin wannan abin alkairi da ki ki gudanar a yau? Abinda zance shine, su ma Allah ya basu ikon gudanar da wannan abin alkairi.

Duk da yake da yawan jarumai maza da mata suna irin wannan abin alkairin, nima da wasu nayi koyi irinsu A Zango, Sani Danja, Ali Nuhu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: