Monday, 16 April 2018




Maketatan Mutane Ne Suka Talauta Al'ummar Nijeriya - Inji Buhari

Home Maketatan Mutane Ne Suka Talauta Al'ummar Nijeriya - Inji Buhari
Ku Tura A Social Media
Maketatan Mutane Ne Suka Talauta Al'ummar Nijeriya - Inji Buhari

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya bayyana cewa Maketatan shugabanni suka talauta al'ummar Nijeriya ta hanyar sace arzikin kasa.

i wannan ikirarin ne a lokacin da 'yan Nijeriya mazauna kasar Birtaniya suka kai masa ziyara a birnin Landon inda ya jaddada cewa gwamnatinsa ta yi kokari wajen maido da Nijeriya kan tafarkin ci gaba idan aka yi la'akari da yanayin da ta karbi mulki daga hannun PDP.

Ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da shirinta na kwato kudaden sata duk da yake ba zai yiwu a gano dukkan kudaden da aka wawure ba inda ya nuna takaicinsa kan yadda aka sace kudaden Nijeriya wanda har sun kasa tsara yadda za su yi rufa-rufa.
©rariya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: