'marasa kunyar 'yan mata dake shigowa sana'ar fim ke ja mana zagi'>>Jamila Nagudu
A wata hira da tayi da bbchausa, tauraruwar fina-finan Hausa, Jamila Nagudu ta bayyana cewa wasu bata garin 'yan matane dake shigowa masana'antarsu daga waje ke sawa ana musu kudin goro ana zaginsu.
Jamila tace zaka ga yarinya ta taso a unguwa bata ganin girman iyayenta da manyan mutane kuma sai tazo masana'antar fim ta samu sa'a a dauketa to anan ma sai ta cigaba da wannan hali nata sai mutane su rika ganin kamar duk 'yan fim haka suke.
Jamila ta bayyana cewa ta taba yin aure kuma tana da da daya.
Jamila ta bayyana cewa tana taka duk wata rawa da aka bata da kyaune saboda sai mutun ya dage ya nuna kwazo sannan za'a kirashi jarumi, mutum ba zai taba zama jarumi ba haka kawai, ta kara da cewa duk wani abu da aka ga tana kuka akanshi a fim ta tabbata idan ace me kallone akawa irin wannan abu to shima zai iya yin kuka.
Jamila ta kara da cewa yawanci yanzu ba sa'anta a masana'antarsu dan da yawa suna kiranta da anti ko Hajiya, a karshe tace ta godewa Allah da irin abubuwa da daukakar da ta samu, inda ta bayyana cewa ba kowane jarumine ya samu irin abinda ta samu ba a sana'ar fim.
0 Comments: