Wednesday, 23 May 2018




Akwai hassada da bakin ciki a masana'antar fim Rahama Sadau

Home Akwai hassada da bakin ciki a masana'antar fim Rahama Sadau
Ku Tura A Social Media
Tauraruwar fina-finan Hausa Rahama Sadau na daya daga cikin wanda suka taka rawa suka kuma bar tarihin da ba za'a taba mantawa dashi a masana'antar fina-finan Hausa ba, tun daga shigowarta masana'antar, cikin kankanin lokaci ta samu daukaka ta kere sa'anninta.

Wani abu da ya faru da jarumar wanda za'a iya kiranshi da koma baya da ta samu,

shine dakatar da ita da akayi a shekarun baya dalilin fitowa da tayi a wani faifan bidiyo da suka yi waka tare da Classiq,

amma sai abin ya zamar mata sanadin kara daukaka, shararren mawakin kasar Amurka, Akon ya kirata, ta kara samun karbuwa a gurin fina-finan kudu.

Duk wanda yake da wata daukaka a tsakanin sa'anninshi ba zai rasa hassada da kishi ba:

Jar umar ta rubuta a dandalinta na sada zumunta da muhawara cewa:
Ba sabon abu bane hassada, bakin ciki da rashin kishin juna a masana'antar fim, musamman tsakanin mata.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: