Iyaye sun kai dansu dan shekaru 30 kara kotu akan ya fita ya bar musu gida su
Wasu iyaye a kasar Amurka sun kai dan su daya tilo dan shekaru talatin kara kotu saboda yazo ya zaune musu a gida baya biya musu kudin haya OK taimaka musu ta kowace irin hanya, sunce shekara takwas kenan suna zaune tare dashi.
Mark da matarshi Christina Rotondos dake zaune a birnin New York n a kasar Amurka, sunce kusan watanni hudu kenan suna baiwa dansu notis akan ya tashi ya basu guri amma yaki ya, sunce sun aikamai a rubuce, kuma har kudi suka bashi yaje ya kama haya amma duk ya kiya.
Sun kara da cewa kuma yaki neman aiki yayi.
Alkalin kotun da suka kai kara dai ya yanke hukuncin cewa Micheal ya tashi daga gidan ya baiwa iyayenshi guri.
Amma bayan kammala shari'ar, Micheal ya fito ranshi a bace ya kuma shaidawa manema labarai cewa baya tunanin alkalin kotun ya karanta bayanan da aka bashi da kyau dan haka be yadda da wannan hukumnci ba, zai daukaka kara.
0 Comments: