Wednesday, 27 June 2018




Kalli wani kambun neman sa'a da Messi ya daura a kafarshi lokacin wasasu da Najeria

Home › › Kalli wani kambun neman sa'a da Messi ya daura a kafarshi lokacin wasasu da Najeria

Post By:

Ku Tura A Social Media
Kalli wani kambun neman sa'a da Messi ya daura a kafarshi lokacin wasasu da Najeria

A lokacin wata tattaunawar da yayi da manema labari, wani dan jarida ya tambayi dan kwallon kafar Argentina Messi ko har yanzu yana sanye da wani kambun neman sa'a da ya bashi lokacin wasan Iceland? Sai messin yace Eh.

Messin ya tattare safar kafarshi inda ya nunawa dan jaridar kambun, hakan ya farune bayan kammala wasa tsakanin Argentina da Najeriya wanda ya baiwa Argentinar nasara da ci 2-1.

Dan jaridar dai ya baiwa Messi wannan kambune wanda yace na neman sa'ane kuma shima matarshi ce ta bashi.

Share this


Author: verified_user