Masanan kimiyya a Ostireliya sun gano wani nau'in maciji da ba a taba ganin irin sa ba
Malaman kimiyyar halitta a jami'ar Queensland ta kasar Ostireliya sun gano wani nau'in maciji da ba a taba ganin irin sa ba.
Daya daga cikin malaman kimiyyar Bryan Fry ya ce sun je wani yanki don gudanar da bincike kan macizan da ke rayuwa a cikin teku inda suka samu wani maciji da ke rayuwa a karkashin kasakuma sun yi mamakin ganin sa.
Fry ya ce, sun gano macijin a tsibirin Cape York kuma yana kama da dangin macizai da ke rayuwa a karkashin kasa.
Masanan Kimiyyar halittar na tunanin jiragen ruwa ne suka turo macijin zuwa gabar teku.
Sun bayyana cewa, ba kasafai ake ganin irin wannan maciji ba.
trthausa.