Manyan sarakunan Najeriya guda 4 da ba su da aure
Sanannen abu ne a kusan kowanni kabila ko addini cewa aure muhimmin abu ne, kuma ita cikar kamalar mutum mace ko namiji, hakan ta sanya aure ya fi zama cancanta ga shuwagabanni, don haka zaka ga da zarar wani ya samu mukami sai yayi aure, ba duka aka zama daya ba, inda a Najeriya aka samu wasu manyan sarakuna dake mulkin manyan masarautu amma basu da aure, ku biyo mu.
Wadannan sarakunan basu da aure har yanzu, duk da suna gudanar da mulkin dubunnan al’umma.
Sarkin Gombe
Sarkin Gombe, mai martaba Alhaji Abubakar Shehu na Uku ya dane mukamin Sarki kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Gombe ne yana shekaru 39 bayan mutuwar mahafinsa, Alhaji Sheu Abubakar kimanin shekaru uku da suka shude.
Sai dai duk da cewa a yanzu haka yana da shekaru 42, amma Sarki Abubakar bai taba aure ba, kuma bashi da mata a ko ina, a duk fadin jihar Gombe da ma Najeriya gaba daya, wanda hakan na damun al’ummar jihar Gombe.
Majiyoyi sahihai sun tabbatar da cewar a yayin da za’a nada shi sarautar Sarkin Gombe, an so a daura masa guda daga cikin yayan Sarkin Musulmi amma abin bai yiwu ba, haka zalika aurensa da diyar Sarkin Dukku, Gimbiya Aisha Musnan saura kiris, amma abin bai yiwu ba.
Amma duk da wannan nakasu, Sarki Abubakar yana da kyakkyawar alaka da jama’ansa, talakawansa na kaunarsa sakamakon taimakon dayake musu.
Sarkin Ife (Ooni Ife)
Sarkin Ife na daga cikin matasan sarakuna a Najeriya, kuma shine shugaban majalisar sarakunan jihar Osun gaba daya, yayi aure har sau biyu, amma auren bai dade ba, aurensa na karshe a ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2016 aka yi, inda ya auri Sarauniya Wuraola Zaynab Otiti Obanor, amma suka rabu a shekarar 2018.
Tun bayan wannan mutuwar aure wanda hatta sadakin daya biya saida aka dawo masa dasu, Ooni mai shekaru 43 bai sake wani auren ba, sai dai ana samun jita jitan cewa ya kusa angwancewa, inda ake danganta shi da Sarauniyar Kyau Tobi Philips.
Sarkin Agbor (Dein Agbor)
Dein na Agbor, Sarkin masarautar Agbor dake jihar Delta, Benjamin Ikechukwu Kiagborekuzi I shine wanda ya zama Sarki tun yana karamin yaro dan shekara 2, 1979 bayan rasuwar mahafinsa, a yanzu yana da shekaru 42 amma shima har yanzu bashi da mata.
Dayake Benjamin ya dade a kasar waje yana karatu, don haka tun bayan dawowarsa Najeriya a shekarar 2001 ake zargin wai buduwarsa baturiya zai aura, amma mambobib majalisarsa sun ce atabau ba zai auri baturiya ba, yar kabilar Agbor zai aura.
Sai dai shima Basaraken yana da girma sosai a idon jama’ansa, suna matukar kaunarsa tare da mutunta shi.
Sarkin Ubulu-Uku (Obi Ubulu-Uku)
Sarkin al’ummar Ubulu Uku dake jihar Delta, Oba Chukwuka Akaeze I ya dare karagar mulki ne a shekarar 2016 yana dan shekara 15 bayan miyagu masu garkuwa da mutane sun kashe mahaifinsa Edward Ofulue III, ma’ana yanzu shekararsa 17, inda ya kwashe shekaru biyu yana mulkar jama’a amma bashi da aure.
Amma a iya cewa karancin shekaru ne suka hana Oba Akaeze aure, don kuwa a yanzu haka yana kasar waje yana karatu, kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.
Naij.com
0 Comments: