Saturday, 10 November 2018




Yan Bindiga Sun Sace Yan Mata Tagwaye Da Ake Shirin Bikin Su

Home Yan Bindiga Sun Sace Yan Mata Tagwaye Da Ake Shirin Bikin Su
Ku Tura A Social Media
An sace wasu ‘yan mata tagwaye lokacin da suke kan hanyarsu ta kai wa ‘yan uwa da abokan arziki ankon bikinsu, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Mataimakin Shugaban karamar hukumar Zurmi Abubakar Muhammad ya ce tagwayen wadanda ake shirye-shiryen aurensu suna cikin mutane bakwai da aka sace a garin Dauran da ke jihar ZamfaraZamfara.

“A tsakanin ranakun Asabar zuwa Lahadi ne aka sace mutanen bakwai – wato maza hudu, mata uku.

“Nan kusa gare mu ma an sace namiji guda, mace guda wato nan Birnin Tsaba ke nan,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: “A garin Moriki an ma an dauki mutum uku da wadansu da aka sace ciki har da wani kansila.”

Har ila yau ya ce an yi magana da masu garkuwa da mutanen kuma sun bukaci a “biya su naira miliyan 100 kafin su sako ‘yan tagwayen.”

Daga nan ya bukaci da a kawo musu dauki don kawo karshen matsalar.

Zamfara tana daya daga cikin jihohin arewacin kasar da ke fama da matsalar tsaro.

BBC HAUSA

Share this


Author: verified_user

0 Comments: