Friday, 12 January 2018




News: An Sallamo Yusuf Buhari Daga Asibiti

Home News: An Sallamo Yusuf Buhari Daga Asibiti

Post By:

Ku Tura A Social Media

Dailypost ta rawaito cewa an sallamo yaron shugaba Buhari, Yusuf Buhari daga asibitin Cedarcrest a yau bayan jinyar da ya yi sakamakon hatsarin babur a Abuja.

shugaba Buhari na musamman kan kafafin sada zumunta, Bashir Ahmad ya tabbatar da samun saukin Yusuf tare da sallamo shi daga asibitin Cedarcrest.

A ranar 26 ga watan Disamba ne aka kwantar da Yusuf Buhari biyo bayan hatsarin babur daya rutsa da shi a Abuja, bayan nan ne aka farfado da shi babban asibitin Cedarcrest inda aka yi masa tiyata, kuma a yanzu haka ya samu sauki sosai har an sallamo shi daga asibitin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: