Babban Abun Da yake Hana Wasu ‘Yan Matan Samun Aure Da Wuri
Bayani na hakika ya tabbatar da cewa sau da yawa wasu ‘yan matan kan fada cikin larurar rashin samun abokin zama sakamakon girman kai, wanda masu hikima kan ce rawanin tsiya, shi kuma Abubakar Imam a cikin littafinsa na Magana Jar ice, ya karasa managanar da cewa, duk wanda ke wulakanta jama’a zai ga iyakarsa. Da yawan ‘yan mata yayin da suka kai wani mataki na girma tauraruwar suna haskawa a wannan lokacin wanda hakan ne yake sa wa samari su yi wo tururruwar zuwa wajen budurwa don zama masoyinta na aure da na nishadi ma. A wannan lokaci ne budurwar ke ganin ta zama tauraruwa wadda hakan yakan sa ta girman kai wajen zabar masoyi na kwarai kuma na gaskiya wanda yake sonta tsakani ga Allah. ‘Yan matan sukan zabi masoyi yayin da suka sami wanda ya fi shi sukan canja akalarsu kan wanda idanuwan su ya gano, haka za su yi ta canzawa har su rasa wanda za su zaba. Girman kai da rudin duniya yakan saka idanuwansu rufe wa su rasa gane ina suka dosa. Ba wani abu ba ne yake janyo hakan illah son rai da kuma son abin duniya shi yake kawo hakan wani lokacin ma da karance-karancen littafin Hausa da yake tasiri cikin zuciyarsu. Da yawa a yanzu sukan dauki buri mai girma su dorawa kansu wanda hakan ko kusa ba zai samu ba, idan kuwa ya samu to! Sai an sha wuya ko kuma a same shi da sauki karshe a sha wahala. Da yawa daga wasu ‘yan mata kan saka wa zuciyarsu cewa lallai sai kyakkyawan saurayi kamar zubin Fulani irin saurayin da ake ba su labari cikin littafin Hausa za su aura. Sai budurwa ta saka wa zuciyarta lallai sai irin wannan namijin za ta aura wanda yake mara makusa kamar shi ya yi kansa, ko kusa babu wannan ba zance babu kwata-kwata ba amma kafin a samu za a dade a ce an samu wanda ya hada komai ba shi da wata makusa kamar yadda na cikin littafin Hausa yake. Haka kuma wasu kan saka wannan a ransu duk saurayin da ya zo sai su ce ba sa so, saboda sun ruga sun bar wa zuciyarsu wannan tsarin. Ko kuma mace ta kudurce cewa lallai sai mai kudi saboda mijin kawarta ko saurayin kawarta mai kudi ne, don haka ita ma sai mai kudi ko kuma ajinta ya wuce ta auri talaka ko wanda sana ‘arsa ba mai girma ba ce, irin wadda duniya za ta san da zamansa ba. Iri-irin wadan nan da ma wasu ra’ayoyin nasu wanda ban ambato su ba, toh! Yakan saka wasu matan girman kai don ba duka ne aka taru aka zama daya ba, sai an amince wa saurayi ringidi- ringidi da zarar wanda ya fi shi ya zo sai zance ya sha bamban. Mata sai kun mun hakuri domin yau shafin nawa naku ne, ki sani cewa yayin da kika tsaya nuna girman kai za a kai ki a baro ki ne komai kyanki. Mata sukan rasa na zaba har lokacin da samarin za su daina zuwa lokacin mace ta huce wannan matakin da tauraruwar tata take haskawa sai kuma ta dawo tana lissafa adadin samarin da tayi tana data sani tun a wancen lokacin ta zaba daya fi mata yanzu gashi tana zaune ana aurar da kannenta tana gani. A cikin hali girman kai wasu sukan kudurce su ba za su auri mai mata ba wani sa in ma har iyaye sukan ba wa yaranau gudun mawa wajen haifar da ruwan idon yayin da a kai ta zaben aka rasa sai a dawo ana addu’ar Allah ya kawo koda me mata uku ne saboda burinsu a lokacin a aurar kar masu zuwa unguwa su rinka ci gaba da zagi ko kuma saka ido a kowanne motsi na yarinyar.
A cewar wasu ‘yan matan zama da sautayi daya tsautsayi ne, gwara su rana kafa har Allah ya sa a dace, sai dai kuma abin takaicin shi ne za ku ga wasu mazan na arziki wadanda suke da niyyar yin aure kuma sunje wajen yarinya da zuciya daya amma ita sai ta ki amincewa da soyayyarsa koda kuwa ba shi da wata makusa a tare da shi ta biye wa samari matasa wadanda ba su da niyyar yin aure a wannan lokacin wato maza ‘yan tayin hira su rudeta su janye zuciyarta da wasu abubuwan wadanda ita a lolacin ba za ta san hakan ba sai ranar da ta yi hankali ko lolacin da ta saninta ya zo. Ina kira ga masoya musamman mata tun da batuna gare ku nake a yau da ku daina girman kai su tsaya su kula wajen zabar miji nagari, don gudun da an sani wata rana wasu mazan sukan zo wa ‘yan mata da abubuwa daban-daban dan janye zuciyarta Wanda a bayan auren mace za ta ga ba hakan yake ba sai kuma tayi da ta sani wane ta zaba sai a lokacin za ta rinka hango halayyar wancen wanda ta bari ta yi da ta sani ta dauke shi, da na sani dai keya ce. Wata ma garin girman kai ta zabo wa kanta wanda kullum zai rinka jibgarta ko kuma wanda zai rinka hanata abinci, dan akwai masu kudin da basa iya fitarwa cikin gidansu basa bawa iyalansu komai sai dai a runka gyara ginin gida ko shi ya tunka dinki yana canjawa ana alhj wane me kudi ne amma fa cikin gidan sa iyalai na kuka ‘yan mata sai a kiyaye. Haka zalika akwai namijin da za ki dabe shi dan gayunsa amma bayan anyi aure sai lamari ya canja wannan dan tsukewar da yake yi yana janyo zuciyarki sai kiga duk ba hakan yake ba sai zai futa yake samun daman yin wanka ma in har zabai futa ba toh ba shi ba wanka kin ga ba labari lamari ya baci sai a kula dan gudun da an sani an zabi me shigar kamala wanda yake sako ta-zarce ana kushe shi ana cewa bai waye ba.
Masoya sai a kula a rinka danne zuciya a nutsu a yi aiki da hankali wajen zabar mijin aure don kar a yi zaben tumun-dare. Sanfuran Kalaman Soyayya Muna son junan mu kuma yanzu mun gama zama daya amma meye lefina dan na mamaye zuciyar kyakykyawa kamarki? Inama ace kikalli mudubi kiga tsabar kyan halittarki dole na riritaki na kula dake domin bazanyi wasa ki kubuceminba N inasan wahalar da nasha harna sameki tabbas ke mai darajace kuma bazan miki kishiyaba Ahankali gashi zuciyata ta kamu da cutar da ke kadaice mai maganinta babu maganar na guje to inama zanje na samu nutsuwa sama da gunki masoyiyata Kece idona yake son kallo a koda yaushe kallon hotonki ya zamammin aiki wallahi ke kyakykyawa ce Wannan zumar ta soyayya zan ci gaba da lasa miki muddin zaki sha daga koramata Ke hasken rana ce dake dusashe duk-kan duhu, da daddare kuwa kece farin wata sha kallo Kuma kece tauraruwar da take haska sararin samaniyar zuciyata Kyallin kyawun fatarki kadai kan haddasar da hargitsin nishadi a zuciya sanda na tuno da hakan Dukkan hakkin soyayya zan baki tunda kin ban ragamarki a hannuna da kuma sanyaya ranki kece zara ni wata Zanso ace kina gefena dakin juya ni zaki gani a damarki Ni na ruga na mallaka kaina gareki komene zan miki bana kokonto tunda na gane kece maisona.
Kinsan walwalarki itace sinadarina na warwasawa. Ka goda Allah domin kuwa kana da babbar bai wa ta kalamai wadda duk wata ‘ya macen data jisu dole su shiga cikin jikinta har ya sata walwala koda kuwa ranta a bace yake lokacin ina alfahari da kai zamowa gwarzo gareni kuma jajirtacce wajen bayyanar da ingantacciyar soyayya gareni me dauke da nishadi. . Copyright
0 Comments: