Wednesday, 5 September 2018




Meyasa Amare ke nuna tsiraici da sunan hoton biki?

Home Meyasa Amare ke nuna tsiraici da sunan hoton biki?

Post By:

Ku Tura A Social Media
Meyasa Amare ke nuna tsiraici da sunan hoton biki?

Wata baiwar Allah ce me suna khadija tayi jan hankali a shafinta na Facebook cewa wai me yasa Amare ke nuna tsiraici da sunan yin hoton biki amma bazaka taba ganin shi angon yayi shigar banza ba a hoton koda yaushe mazan zaka gansu da dogayen kaya da hula irin na al'ada.

Ta kara da cewa kuma abin ban haushi idan aka shirya liyafar cin abincin dare haka amaryar zata shigo irin wadannan kaya tsakanin yan uwanta da surukanta dda abokan mijin nata kuma har a kirata ita da angon suyi rawa kala-kala a gaban jama'ar da suka taru a gurin. Wannan dai ba addini bane kuma ba al'adar mu bace.

Ta kuma kara da cewa shin wai shi angon baya kishin matar tasfhi ne? Kuma ba cewa akayi ba zai zama sutura a gareta ba? To yaya akayi ya barta take nuna tsiraici haka?
Ita kuma amaryar wa takeso ta nunawa jikinta?.


Ya kamata dai a gyara:
Allah ya shiryemu. Amin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: